Taron Osinbanjo da shugabanin kudu da arewa

Taron Osinbanjo da shugabanin kudu da arewa

- Osinbanjo yace doka zata hukunta duk wanda aka kama da laifin tada zaune tsaye

- Dokar Najeriya ta ba kowane dan kasa daman zaman a inda yake so

- Najeriya zata cigaba da zama a matsayin ta na kasa daya

Bayan cece-kuce da ake tayi tsakanin kabilun da ke arewaci da kudancin Najeriya. Shugaban kasa mai rikon kwarya Osinbanjo ya kira taro da shugabnin bangarorin domin a cinma matsaya da zata wanzar ta zaman lafiya. Manufar taron dai shine domin kowa ya fada albarkacin bakinsa da bada shawarwari da kawo hadin kan mutane Najeriya da zaman lafiya dawamame.

Taron ya samu hallartan masu ruwa da tsaki a harkan tsaro na Najeriya, sun tattauna akan yunkurin wasu kungiyoyi daga kudu na ballewa daga Najeriya da kuma takwarar sun a arewa da suka basu wa’adi na fice wa daga arewan.

KU KARANTA KUMA: An dakile shirin kai hare haren ta'addanci a ranar Sallah

Taron Osinbanjo da shugabanin kudu da arewa

Taron Osinbanjo da shugabanin kudu da arewa

Daga karshen taron a cin ma matsayu guda (5) biyar :

1. Yin tir da duk wasu maganganu da ka iya tada zaune tsaye ko raba kan jama’a a arewaci da kudancin Najeriya.

2. Jaddada kudin tsarin mulkin Najeriya da yaba kowane dan kasa daman zama a kowane bangare da kasar ba tare da nuna masa kyama ko tsangwama ba.

3. Babbance wa tsakanin yanci na fadin ra’ayi da dokar kasa ta ba kowane mutum da kuma kallamen batanci da ka iya tada hankali da kawo rabe-raben kai na jama’a.

4. Ya zama dole a tunkari duk wata matsala da ta taso komin rashin dadin ta, a maimakon ayi ta kakaucewa ana barin matsalan tana zama fitina babba.

5. Akwai bukatan duk shugabani da masu fada a ji daga kowane bangare ko jami’iya suyi amfani da damar da suke dashi wajen hada kan jama’a da kira na zaman lafiya.

Shugaban kasa mai rikon kwaryan ya cigaba da cewa

Muna sane da duk matsalolin da kowane bangaren kasan nan ke fama dashi. Kowa na da abin da ke cin masa tuwo a kwarya amma ya zama dole mu gabbatar da matsalolin namu a hanyar da ta dace ba tare da tada hankali ba.

“Dukkan mu mun amince cewa zamu zauna lafiya a kasa guda … ya kamata mu tabbatar cewa kasar mu ta zauna lafiya a matsayinta na kusa guda daya mai dorewa."

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel