An dakile shirin kai hare haren ta'addanci a ranar Sallah

An dakile shirin kai hare haren ta'addanci a ranar Sallah

- Hukumar DSS ta sanu nasarar damke wasu 'yan ta'adda dake shirin kai hare-hare a jihohin Arewa a lokacin karamar sallah

- Jami'an hukumar sun kama biyu daga cikin 'yan ta'addan da ake zargi da shirin kai hare-haren

Hukumar binciken sirri wato DSS, ta sanar da samun nasara gurin damke wasu ‘yan ta’adda da ke shirin kai jerin hare-hare a garuruwan Sakkwato, Kano, Kaduna da kuma Maiduguri, a lokacin da ake bukukuwan karamar Sallah.

Jami’an hukumar sun kame biyu daga cikin wadanda ake zargin, Yusuf Adamu da Abdumuminu Haladu da safiyar ranar Juma’a, 23 ga watan Yuni a garin Sakkwato, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Cikin sanarwar da ya fitar a Juma’ar nan, kakakin hukumar ta DSS Tony Opuiyo, ya ce tun a makwannin da suka gabata suka samu bayannan sirri da ke cewa, ‘yan ta’addan na shirin kai harin bam a sassan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Dino Melaye: Daga mai bakin tsiya ya koma wanda kujerar sa ke lilo

An dakile shirin kai hare haren ta'addanci a ranar Sallah

An dakile shirin kai hare haren ta'addanci a ranar Sallah

A ranar 20 ga watan Yuni NAIJ.com ta samu labarin cewa hukumar binciken sirrin ta kama wani kwararre wajen hada bama bamai, mai suna Bashir Mohammed a Shekar Madaki da ke karamar hukumar Kumbotso jihar Kano.

Yayin gudanar da bincike kuma jami’an na DSS sun gano manyan bindigogi kirar AK 47 guda takwas, bindigogi masu sarrafa kansu 20, bama-baman gurneti 27, sai kuma alburusai 793.

Har ila yau jami’an sun kwace tukunyar gas guda, komfutar laptop 3, sai kuma, mota daya da babur din hawa.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun majistare na Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun majistare na Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel