Wani attajiri ya fitar da fursunoni 30 ta hanyar biya masu kudin tara a jihar Gombe

Wani attajiri ya fitar da fursunoni 30 ta hanyar biya masu kudin tara a jihar Gombe

- Alhaji Abubakar Habu Mu'azu da ke jihar Gombe ya fitar da wasu fursunoni 30 daga gidan kaso

- Mu'azu yace ya yi hakan ne domin albarkacin watan Ramadan

- Mataimakin Comptroller ya ce sake fursunonin zai taimaka wajen rage cinkoso a gidan kason

Albarkacin watan Ramadan, wani mai hannu da shuni da ke jihar Gombe, Alhaji Abubakar Habu Mu'azu, a ranar Alhamis, 22 ga watan Yuli ya ba wata kungiyar musulunci wanda aka sani da Da'awah Relief Foundation goyon baya inda ya biya wa wasu fursunoni 30 domin a sake su daga gidan kaso a Gombe.

An sako ‘yan fursunonin ne daga gidan yari da ke Gombe ta tsakiya bayan da aka biya masu wasu kudaden tara a lokacin da kungiyar ta ziyarar gidan yarin a karkashin jagorancin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.

NAIJ.com ta ruwaito cewa Sheikh Daurawa ya bayyana cewa an sako 'yan fursunonin ne bayan da Habu Mu'azu ya biya kudin tarar aka a kansu.

A lokacin da ya ke tofa albarkacin bakinsa malam Habu Mu'azu ya ce yayi wannan alhaeri ne albarkacin watan Ramadan da kuma taimaka wajen an rage cinkoso a gidan yarin.

Ya ce: "Mafi yawa daga cikin fursunonin sun kasance a gidan yari domin gazawarsu biya adadin kudin tarar de kansu a matsayin wata hukumcin, al’amarin da yasa na yanke shawarar shiga tsakani ta hanyar biyan kudaden a cikin wannan watanmai alfarma na Ramadan da kuma taimaka wajen rage cinkoso a gidan yarin. "

KU KARANTA: Babban hadimin gwamnan jihar Taraba ya yanke jiki ya fadi, ya kuma cika nan take

Yayin da yake yabawa Habu Mu'azu ga karimcin, mataimakin Comptroller Abubakar Muhammad Abdu, ya ce sake fursunonin zai taimaka wajen rage cinkoso a gidan yarin. Abubakar ya kuma shawarci mutanen da su kasance masu halaye na gari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel