'Yan sanda sun fake a matsayin masu neman sassan jikin mutane, wani boka ya kawo musu kan mutum

'Yan sanda sun fake a matsayin masu neman sassan jikin mutane, wani boka ya kawo musu kan mutum

- Ya ce ya dade yana ajje da kokon kan mutum

- Yana sayar da sassan jikin mutane kan farashi mai tsada

- Yan sanda sun fake kamar yan gari suka burma shi

A cikin garin Ikko, an sami wani boka mai suna Toseni Hussein, wanda ake zargin yana sayar da sassan mutane ne, da aka yi dabara aka burma shi, sai kawai gashi yana sayar da kan mutum ga masaya, wadanda bai sani ba ashe yan-sanda ne suka yi masa talala.

Da aka tambaye shi yadda aka yi ya sami kan mutum sai yace ai tun shekarun baya ya tsinci kan yana sabo, ya dauko wai ya adana don amfanin nan gaba.

'Yan sanda sun fake a matsayin masu neman sassan jikin mutane, wani boka ya kawo musu kan mutum

'Yan sanda sun fake a matsayin masu neman sassan jikin mutane, wani boka ya kawo musu kan mutum

An dai tuhumi shi Malam Hussein da tsafi da kashe mutane, zargi da ya musanta, amma ya yarda cewa yana sayar da sassan mutane a kan kudi da ya kama daga dubu dari da hamsin na naira zuwa miliyan daya, yace farashi ya dangana da wanne bangare na jikin mutum ake bukata.

"A shekarar 2012 na tsinci kan mutum a shagamu ta jihar Ogun, lokacin kan yana sabo, na dauka na kawo gida tunda dama ni boka ne mai bada magani, kuma ina taimakon jama'a, amma daga baya sai na koma harkar sayar da sassan jikin mutane, domin yafi kawo kudi," cewar sa.

'Yan sanda dai a jihar sun sami labarin wannan ja'iri, suka yi masa waya kan suna son sassa daban daban na mutane, inda ya amsa ya bada farashi, ya kuma kawo, su kuwa suka damke shi.

"Ban san yansanda ne nayi ciniki da su ba' yace, bayan da ya shiga hannu."

Malam Danladi Galadanci, mataimakin kwamishinan 'yan sandar jihar, ya tabbatar da hakan, ya kuma ce zasu muka shi ga kotu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel