Wata mata ta sayi jaririn wata 10 kudi N650,000 a jihar Imo

Wata mata ta sayi jaririn wata 10 kudi N650,000 a jihar Imo

Wata bazawara wami suna Ogechi Chukwuocha, ta bayyana cewa tsananin bukatan da na mijin da takeyi ya ingizata sayan jaririn wata 10 kudi N650,000 a jihar Imo.

Ogechi Chukwuocha,tayi wannan bayani ne a hedkwatan hukumar yan sandan da ke Owerri inda aka garkameta tare da wadansu kuma aka mikawa iyayen jaririn kayansu.

Sauran da aka garkame sune Calister Igwe da Chimezie Okafor,wanda akayi cinikin da su.

Bazawarar tace “ Mijina yam utu ne kuma bani da yaro. Ban san sato jariri akayi ba. Na sayi jaririn N650,000. "

Wata mata ta sayi jaririn wata 10 kudi N650,000 a jihar Imo

Wata mata ta sayi jaririn wata 10 kudi N650,000 a jihar Imo

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Andrew Enwerem, yace an kwato yaron ne a karamar hukumar Orlun jihar Imo.

Enwerem yace, “ An sace yarone ranan 15 ga watan Yuni kuma an cetoshi ranan 20 ga watan. Mun samu rahoto daga mahaifiyar yaron cewa an sace jaririnta na wata 10.

KU KARANTA:

“Tace ta baiwa wata mata mai suna Mrs. Favour Nwokem jaririn ne ta rike mata kafin ta amshi abu cikin daki, amma kafin ta fito, Favour ta arce da jaririn. Da wuri hukumar ta bisu kuma ta damke 3 daga cikinsu, amma har yanzu ba’ a kama Mrs. Favour Nwokem ba."

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel