Ban karbi cin hancin naira miliyan 100 ba don dakatar da binciken Sarkin Kano – Kakakin majalisar dokokin Jihar

Ban karbi cin hancin naira miliyan 100 ba don dakatar da binciken Sarkin Kano – Kakakin majalisar dokokin Jihar

- Kabiru Rurum ya karyata rahoton cewa ya karbi cin hanci na naira miliyan 100 don hana ci gaba da binciken sarki Sanusi

- Ya ce hakan ba gaskiya bane sannan kuma zai kafa wata kwamiti a majalisar da zata binciki wannan korafi

Kakakin majalisar Dokokin jihar Kano Kabiru Rurum ya karyata rahoton wata gidan Jarida da ta rubuta wai ya karbi cin hancin naira miliyan 100 domin ya tilastawa majaisar ta dakatar da ci gaba da binciken Sarkin Kano Muhammadu Sanusi.

Rurum ya ce hakan ba gaskiya bane sannan kuma zai kafa wata kwamiti a majalisar da zata binciki wannan korafi.

KU KARANTA KUMA: Yan Shi’a zasu yi gangamin tattakin tunawa da ranar Qudus a yau Juma’a

Ban karbi cin hancin naira miliyan 100 ba don dakatar da binciken Sarkin Kano – Kakakin majalisar dokokin Jihar

Ban karbi cin hancin naira miliyan 100 ba don dakatar da binciken Sarkin Kano – Kakakin majalisar dokokin Jihar

Ya kara da cewa idan har aka fara binciken dole sai wannan gidan jarida da ta ruwaito labarin ta bayyana a gabanta.

Daga karshe ya bayyana cewa irin haka shiri ne na makiyansa amma babu kamshin gaskiya a cikinta.

Mukaddashin shugaban Kasa Yemi Osinbajo da wadansu jiga-jigan ‘yan Najeriya ne suka roki majalisar ta gwamnan jihar Abdullahi Ganduje domin majalisar ta dakatar da binciken.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel