Kungiyar ýan ta’adda ta tashi Masallaci mai shekaru 800 ta hanya harba bamabamai (HOTUNA)

Kungiyar ýan ta’adda ta tashi Masallaci mai shekaru 800 ta hanya harba bamabamai (HOTUNA)

- Kungiyar yan ta'adda ta lalata babban Masallacin Mosul

- Kungiyar ta zagaye masallacin da hasumiyarsa da bamabamai ne

A ranar Laraba 21 ga watan Yuni ne kungiyar yan ta’adda mai suna ISIS tayi rugu rugu da wani katafaren Masallaci, Masallacin Al-Nuri mai shekaru 800 a duniya a garin Mosul dake kasar Iraqi.

NAIJ.com ta ruwaito cewar mayakan ISIS sun tada Masallacin tare da hasumiyarsa, kamar yadda hukumomin tsaron Iraqi suka shaida.

KU KARANTA: Tabdijam! Wani Sarki ya hada akidar addinin Musulunci, Kirista da na gargajiya duka (Hotuna)

Haka zalika shima Kaakakin rundunar sojojin Amurka Kanal Ryan Dillon ya shaida cewa “ISIS sun lalata Masallacin Al-Nuri, ba mu muka kai masa hari ba, bamu kai hari a wajen ba.”

Kungiyar ýan ta’adda ta tashi Masallaci mai shekaru 800 ta hanya harba bamabamai (HOTUNA)

Masallacin Al-Nuri

A shekara 1172 ne aka gina wannan Masallaci a zamanin Sar Nur al-Din Mahmoud Zangi, kuma a cikin wannan Masallaci ne shugaban ISIS, Abu Bakr Al-Baghdadi yayi ikirarin kalifancin musulman Duniya gaba daya.

Kungiyar ýan ta’adda ta tashi Masallaci mai shekaru 800 ta hanya harba bamabamai (HOTUNA)

Bayan sanya bamabaman

Sai dai mutanen garin Mosul sun yi mamakin yadda ISIS ta rusa Masallacin da kanta, wani mazaunin garin, Hassan Hassan yace “Da ya zama abin kunya a wajen ISIS idan da Sojoji sun kwaci Masallacin lafiya lau, don haka ne suka rusa shi, domin borin kunya.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel