Riba biyu: Ta maido da N19,000 kuɗin tsintuwa, an bata tukuicin N200,000

Riba biyu: Ta maido da N19,000 kuɗin tsintuwa, an bata tukuicin N200,000

- Wata yarinya ta samu tagomashi bayan tayi wani aikin kirki

- Yarinyar ta mayar da Naira 18,000, ta samu 200,000

An cika ma wata yarinyar mai shekaru 19, dalibar makarantar Sakandari, Samson Omobolake alkawarin tukuicin N200,000 da aka yi mata sakamakon aikata wani aikin kirki.

A wancan lokacin NAIJ.com ta kawo muku rahoton yadda Omobolake wanda take karatu a makarantar sakandari dake jihar Ogun ta tsinci wani jaka dake makare da tsabar kudi har Naira 18,000, amma ta nemi mai shi muma ta mayar masa.

KU KARANTA: Yan Shi’a zasu yi gangamin tattakin tunawa da ranar Qudus a yau Juma’a

Yarinyar ta mayar da kudin ne ga bankin FCMB reshen garin Sagamu na jihar Ogun, domin su nemi mai kudin su ba shi, sai dai dayake kayan ta sun tsinke a gindin kaba, ashe babban daraktan bankin na sashin kudu maso yammacin kasar nan Babatunde Onadeko ya kai ziyarar aiki wannan banki a ranar, daya ji abinda yarinyar tayi, sai ya cika da mamaki.

Riba biyu: Ta maido da N19,000 kuɗin tsintuwa, an bata tukuicin N200,000

Daliba Omobolake

Daga nan ne fa yayi alkawarin bata tukuicin naira 200,000, inda a jiya ne ya cika mata wannan alkawari, a gaban sauran daliban makarantar, sa’annan ya gabatar da jawbai ga daliban kan halin kirki da kasnacewa yan kasa na gari.

Riba biyu: Ta maido da N19,000 kuɗin tsintuwa, an bata tukuicin N200,000

Dalibar da malamanta

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Najeriya giwar Afirka

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel