Tabdijam! Wani Sarki ya hada akidar addinin Musulunci, Kirista da na gargajiya duka (Hotuna)

Tabdijam! Wani Sarki ya hada akidar addinin Musulunci, Kirista da na gargajiya duka (Hotuna)

- Sarkin garin Ife na jihar Osun yace shi baya nuna bambamcin addini

- Sarkin yace shi Musulmi ne, kuma Kirista, kuma yana bautan gargajiya

Babban Sarkin yarbawa, na masarautar Ife, Ooni Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi ya bayyana cewa shi fa bashi da matsala da addinai, don haka duka na shi ne, kuma shima nasu ne.

Jaridar Daily Post ta ruwaito Adeyeye yana bayyana cewar shi fa bai ga wani abin kyama tattare da addinin gargajiya ba, inda ya kara da cewa Allah daya ne, amma ana bauta masa ta hanyoyi daban daban.

KU KARANTA: An daina zaɓe a yankin kudu maso gabas, har sai an bamu ƙasar Biyafara –Inji Nnamdi Kanu

Sarkin yace shi mabiyin addinin gargajiya ne, amma an haife shi a cikin addinin Kirista, kuma yana bauta irin ta Musulmai.

Tabdijam! Wani Sarki ya hada akidar addinin Musulunci, Kirista da na gargajiya duka (Hotuna)

Sarki a Masallacin Idi

“Ina zuwa Masallaci in yi sallah, ina je coci in yi bauta, kuma duk da haka ni dan addinin gargajiya ne.” inji Sarki Adeyeye.

Tabdijam! Wani Sarki ya hada akidar addinin Musulunci, Kirista da na gargajiya duka (Hotuna)

Sarkin a Coci

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Sarkin yana fadin haka ne a wata hira da yayi da wata yar jarida mai taken Osusu Show.

Tabdijam! Wani Sarki ya hada akidar addinin Musulunci, Kirista da na gargajiya duka (Hotuna)

Sarkin a wajen bautan gargajiya

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana yi ma sanata kiranye

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel