Biyafara: Maganganun Kwankwaso sun jefa sa cikin matsala

Biyafara: Maganganun Kwankwaso sun jefa sa cikin matsala

– Kalaman Sanata Rabi’u Kwankwaso sun jefa su cikin matsala

– Kwankwaso yace bai dace a kama masu kira a kora Inyamurai ba

– Irin su Balarabe Musa sun dura kan tsohon Gwamman

Kungiyar Ohanaze ta kudu ta soki tsohon Gwamna Kwankwaso. Ohanaze tace da wala-kin cikin maganar Sanatan na Kano. Chuks Ibegbu yace babu wanda ya fi karfin hukuma.

Biyafara: Maganganun Kwankwaso sun jefa sa cikin matsala

Kwankwaso yayi magana game da Biyafara

Kungiyar Ohanaze ta soki kalaman tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Kwankwaso inda tace akwai kulalliya a cikin maganganun na sa. Kwankwaso dai yace bai dace a kama matasan nan da su kayi kira a kora Inyamurai daga Arewa ba.

KU KARANTA: An yi wa mutane kisan kiyashi a Taraba

Biyafara: Maganganun Kwankwaso sun jefa sa cikin matsala

Kalaman Kwankwaso kan Inyamurai sun tada kura

Ohanaze ta bakin Chuks Ibegbu tace babu fa wanda ya fi karfin dokar kasa don haka ma wannan maganar ba ta taso ba inda ta gargadi masu kokarin tada hankalin. Haka tsohon Gwamnan Kaduna Balarabe Musa ya soki kalaman Sanatan.

Sanata Kwankwasi ya ba Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai shawarar matakin da ya kamata ya bi wajen kawo karshen rikicin da ke nema ya barke tsakanin Inyamurai da ‘Yan Arewa, yace tattaunawa ce hanyar zaman lafiya.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An maida Garin su Nnamdi Kanu wani Qudus

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel