'Abin da yasa nake rikici da Gwamna na Yahaya Bello na Kogi' Dino Melaye

'Abin da yasa nake rikici da Gwamna na Yahaya Bello na Kogi' Dino Melaye

- Rashin biyan mai’aikata albashi da pansho ne dalilin rikici na da gwamna Bello

- Ni abin da nake so kawai shine jagoranci na gari – Dino

- Tun hawan Bello kujeran mulkin Kogi, wahalhalu kawai ke dabaibaye mutanen Kogi- Dino

Senata Dino Melaye wanda ke wakiltan kogi ta yamma yace rashin biyan albashin mai’aikata da pansho ne dalilin da yasa suke samun sa-in-sa da gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello.

Dino ya ci gaba da cewa, gwagwarmayar sa yana yi domin kare mai’aikatan Jihar kogi da yan pansho wanda ke cikin matsanancin hali a dalilin rashin biyan albashi da pansho har na wata 15 da gwamnan yayi.

A wata hira da Dino yayi da yan jarida a garin Abuja a ranar Alhamis, senatan yace rikicin sa da gwamna Yahaya Bello ya samo asali ne bayan gwamnan ya nuna halin ko in kula bayan kulle Jami’an da ke Jihar, da Kwallejin malunta ta Jihar har ma da kwallejin kimiya da fasaha.

'Abin da yasa nake rikici da Gwamna na Yahaya Bello na Kogi' Dino Melaye

'Abin da yasa nake rikici da Gwamna na Yahaya Bello na Kogi' Dino Melaye

Ya cigaba da cewa likitocin Jihar ma duk sun tafi yajin aiki saboda rashin biyan su albashi da paansho da gwanmar baya yi.

“Gwamna Bello Yahaya ya karbi naira biliyan 20 daga gwamnatin tarayya a matsayin kudin agaji amma bai biya albashin mai’aikatan ba” Inji Dino

“Ya kuma sake karban naira biliyan 11 a cikin bashin kungiyar Paris amma duk da hakan ya ki biyan mai’aikatan.

“Ni kawai abin da nake bukata shine Jagoranci na gari daga gwamnati.

“Yara basu iya zuwa makarantu, masu hayya basu iya biyan kudin hayyan nasu, Wahalar ta isa haka! Mutanen jihar Kogi sun gaji da irin wannan rashin adalcin na gwamnatin Yahaya Bello.

“Tun hawan Yahaya Bello kan karagar mulkin jihar da kuma Taofiq Isah a matsayin shugaban riko na kananan hukumomi, wahalhalu iri-iri duk suka dabaibaye rayuwar mutanen jihar Kogi.”

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel