An tura karin jami'an tsaro jihar Taraba

An tura karin jami'an tsaro jihar Taraba

- Mukaddashin shugaban kasa ya aike da karin jam'ian tsaro jihar Taraba

- Fada ya sake kacamewa tsakanin Fulani da 'yan kabilar Mambila

- An yi hasarar dukiyoyi da rayuka da dama

Mukaddashin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bukaci aikewa da karin jami'an tsaro wasu garuruwa da kauyukan jihar Taraba a arewa maso gabashin kasar.

A farkon makon nan ne wani sabon rikici ya sake barkewa tsakanin Fulani da 'yan kabilar Mambila a karamar hukumar Sardauna, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama.

KU KARANTA KUMA: Yan Shi’a zasu yi gangamin tattakin tunawa da ranar Qudus a yau Juma’aYan Shi’a zasu yi gangamin tattakin tunawa da ranar Qudus a yau Juma’a

An tura karin jami'an tsaro jihar Taraba

An tura karin jami'an tsaro jihar Taraba

A ranar Alhamis ne mukaddashin shugaban kasa ya yi wani taron gaggawa da Gwamnan Jihar ta Taraba Darius Dickson Ishaku, da kuma manyan hafsoshin tsaron kasar kan yadda rikicin ya ke kara kamari.

Har ila yau, Farfesa Osinbajo ya yi Allah-wadai da masu tada zaune tsaye, inda ya ce za a hukunta duk wadanda aka samu da laifi.

Osinbajo ya ba da umarnin aika wa da bataliya daya ta sojoji da 'yan sanda da sauran jami'an tsaro wuraren da rikicin ya shafa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel