Najeriya zata fara fitar da doya kasashen Turai

Najeriya zata fara fitar da doya kasashen Turai

- Daga karshen watan nan Doya zata zama baturiya

- Kasashen turai da Amurka zasu karbi bakuncin Doya

- Manoman Najeriya zasu dara

Ministan noma Cif Audu Ogbe ya bada albishir na cewa doyar najeriya zata fara shiga kasuwannin kasashen Turai da Amurka, kuma daga 29 ga wannan watan Tan tubu saba'in ne za'a kai kasashen.

A cewar ministan ta hannun hadimin sa na yada labarai, Kwantena ukku ce cike fal da doya zata bar gabar tekun Najeriya, guda daya zata je kasar Birtaniya, kwantena biyu kuma zasu wuce Amurka, don shiga kasuwanni.

Najeriya zata fara fitar da doya kasashen Turai

Najeriya zata fara fitar da doya kasashen Turai

Ministan ya kuma yi kira ga masu tantance kaya a legas, da kada su tsawwalawa manoma kudin fiton doyar saboda a sami saurin fita da kayan don habaka tattalin arzikin kasar Najeriya, wanda tuni ya komade.

'Mai na fetur bazai baiwa samarin mu aikin yi da yawa ba, shi ko noma zai dauki daukacin matasan mu aiki, ya ciyar da kasa, ya kuma basu wani dan abin hannu na kashewa', Inji Minista Audu Ogbe.

Ya zuwa yanzu dai ba'a san ko turawa ne zasu fara cin doya da sakwara ba ko kuwa 'yan Najeriya mazauna can kasashen ne suke son su ci abinci irin na gida. Dama dai akan sami kayan abinci na gida Najeriya a wasu kasashen waje, amma sai uwar tsada.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel