Assha! Sabuwar tashar jirgin ruwa ta Kaduna ta gamu da babban cikas

Assha! Sabuwar tashar jirgin ruwa ta Kaduna ta gamu da babban cikas

- Gwamnatin Najeriya ta ce rashin kyawun hanyoyi ne suka hana ta kaddamar da tashar jirgin ruwa ta kan tudu a garin Kaduna.

- Da yake jawabi jim kadan bayan zagayen gani da ido game da tashar jirgin ruwa ta kan Tudu a garin Kaduna, ministan sufuri na tarayyar Najeriya Rotimi Amechi ya ce za a kaddamar da wannan tashar tudun ne kawai idan an kammala gina hanyoyi.

NAIJ.com ta samu labarin cewa ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jihar da su jira a kammala gina hanyoyin da kuma hauhawar hada- hada a tashar kafin mukaddashin shugaban kasa ko shugaban kasa ya je ya kaddamar da aikin, domin idan babu hanyoyi babu yadda mutane za su iya daukar kayayyakinsu idan an kawo.

Assha! Sabuwar tashar jirgin ruwa ta Kaduna ta gamu da babban cikas

Assha! Sabuwar tashar jirgin ruwa ta Kaduna ta gamu da babban cikas

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-rufa’i dake cikin tawagar gani da idon ta ministan harkokin sufurin, ya bayyana cewa akwai riba ainun da gwamnatin jihar Kaduna da kuma al’umar jihar za su iya ci idan aka kaddamar da wannan tashar ta kan tudu a babban birnin jihar.

Ya ce zai ragewa ‘yan kasuwa dawainiyar zuwa Lagos domin dauko kaya.

A cewarsa, dukan abinda mutum zai iya yi a Lagos, zai iya gudanarwa a nan Kaduna, saboda haka wannan zai kawowa ‘yan kasuwar jihohin arewa sauki. Banda haka kuma za a dauki ma’aikata aiki da yawa, wanda yana daya daga cikin muhimman dalilan da yasa gwamnatin jihar ke taimakawa wajen ganin an gama aikin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel