Madalla! Gwamnatin jihar nan ta Arewa za ta gina gidaje 1,000 domin al'ummar ta

Madalla! Gwamnatin jihar nan ta Arewa za ta gina gidaje 1,000 domin al'ummar ta

- Gwamnatin jihar Neja tare da hadin gwiwar wani kamfanin Italiya da ke Nijeriya za ta gina gidaje har guda 1,000 akn kudi Naira biliyan 8.

- Tuni dai gwamnatin ta Neja ta sanya hannu akan yarjejeniyar wannan muhimmin aiki da kamfanin mai suna Italworks Nigeria Limited.

NAIJ.com ta samu labarin cewa babban Manaja hukumar samar da gidaje ta jihar Neja, Ahmad Abdullahi ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Abdullahi ya ce “Tuni dai gwamnatin jihar Neja ta samar da fili mai fadin hekta 91 a karamar Paikoro a kan titin Minna zuwa Abuja inda a nan ne za a gina gidajen”.

Abdullahi ya ci gaba da cewa: ” A yayin da gwamnati ce za ta samar da filin da za gudanar da wannan aiki, kamfanin Italworks ne zai dauki nauyin gabatar da aikin da ake sa ran zai magance matsalolin rashin muhalli da ake fuskanta a jihar”.

Madalla! Gwamnatin jihar nan ta Arewa za ta gina gidaje 1,000 domin al'ummar ta

Madalla! Gwamnatin jihar nan ta Arewa za ta gina gidaje 1,000 domin al'ummar ta

Shi Babban Darakta na kamfanin Italworks, Mista Gaetano Crisa ya ce “Za a fara wannan aiki ne a watan Yuli (wata mai kamawa) kuma aikin zai samawa dubunnan matasa aikin yi”.

Crisa ya ce “Gidajen za su zama masu dakuna biyu da masu dakuna uku kuma za su gina gidaje masu inganci”.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel