'Yan siyasa biyar da ka iya ceton Dino daga fuskantar kiranye

'Yan siyasa biyar da ka iya ceton Dino daga fuskantar kiranye

- Wane zai iya ceto Dino Melaye?

- Dino Melaye ya zargi gwamna Yahaya Bello da hannu a cikin yunkurin tsige shi

- Jama'ar Kogi west sunce Dino ya dawo gida

Senata Dino Melaye dai ba boyeyen dan siyasa bane a Najeriya saboda mutum ne wanda ya sha kwaranniya iri-iri tun shigar sa Majalisan datijan. A halin yanzu dai yana gab da ya rasa kujeransa a dalilin kai karansa da mutanen da yake wakilta wato (kogi west) sukayi a wajen hukumar zabe na kasa mai zaman kanta wata INEC. A takardan da mutanen suka aike wa hukumar zaben sun tuhumi Dino da halin battanci da rashin ingantantaciyar wakilci.

A bangarensa Senato Dino yace wannan barazana ce kawai kuma ya tuhumi gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello a matsayin wanda yake yi masa zagon kasa. A yayin da yan Najeriya sun kalmashe kafafuwansu suna kallon yadda baddakalar zata kare, akwai wasu 'yan siyasa da ake tsamanin za su iya ceto Dino daga wannan rikita-rikita da ya shiga, wannan yan siyasan kuwa sune;

KU KARANTA KUMA: Ta tabbata: INEC ta sanar da Dino Melaye cewa kwanakin shi sun kusa karewa

'Yan siyasa biyar da ka iya ceton Dino daga fuskantar kiranye

'Yan siyasa biyar da ka iya ceton Dino daga fuskantar kiranye

1. Sanata Bukola Saraki: Saraki dai shine shugaban majilisan na takwas kuma uban gida ne a wajen Dino. Abotar nasu tasamo asali tun kafin Saraki ya zama Shugaban Majalisan. A lokacin da Saraki ke fuskantar bincike da tuhuma daga kotun da'ar ma'aikata, Dino yana daya daga cikin wanda ya mara ma Sarakin baya. Akwai yiwuwar uban gidan nasa shima ya taimake shi yanzu.

2. Sanata Ike Ekweremadu: Ekweremadu shine mataimakin shugaban majalisan dattawa. Duk da kasancewar sa dan jami'iyar PDP, an san shi da hada karfi da karfe da masu fada a ji a majalisan domin cin ma burinsa. Akwai hasashen cewa zai iya sa baki a maganan.

3. Abubakar Atiku: Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya dai aboki na Saraki. Yana iya taimaka ma yaron abokinsa musamman tunda yana da niyyar fitowa takarar shugabancin kasa a shekara ta 2019. Idan ya taimaka ma Dino, shima Dino da Saraki suna iya taimaka masa wajen cin ma burinsa.

4. Ibrahim Babangida: A watan Mayu na wannan shekaran, Saraki da Dino sun kai ziyara zuwa gidan tsohon shugaban kasan a gidansa na Minna. Wannan ziyarar baza ta rasa nasaba da zaben shekara ta 2019 da ke zuwa ba. Tsohon Shugaba Babangida yana iya yunkurin ceto Dino saboda allakar su da mai gidan sa Saraki.

5. Jiga-Jigan APC a Majalisa: Duk da dai ba dukka senatocin APC ke shirri da Dino ba, suna iya hada kai don ceton nasa domin hausawa sunce hanun ka baya rubuwa ka yanke shi ka yarda.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel