Rundunar yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane dauke da wayar salular wani dan majalisar Tarayya

Rundunar yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane dauke da wayar salular wani dan majalisar Tarayya

- Rundunar ‘yan sanda jahar Katsina ta ce ta samu nasarar cafke wasu rikakkun masu garkuwa da mutane tare da fashi da makami su uku a kan titin Jikamshi zuwa Yashe a karamar hukumar Musawa da ke jahar.

- Kwamishinan ‘yan sandan jahar, Adullahi Usman shi ya bayyana haka a wani taron manema labarai a jiya Alhamis.

Ya ce wadanda aka kama sun tabbatar da cewa sun dade su na addabar jama’ar yankin da sace sacen mutane da fashi da makami.

An kama su dauke da kwamfuta samfurin laptop, tsabar kudi Naira dubu dari uku da hamsin da Kudaden waje da ba a bayyana adadinsu ba, sai kuma wayoyin salula guda 19.

NAIJ.com ta samu labarin cewa kwamishinan ya ce da suka matsa bincike sun gano cewa daya daga cikin wayoyin mallakar wani dan majalisar tarayya ne, wacce suka bayyana cewa sun samu wasu ‘yan watannin baya da aka yi garkuwa da shi.

Rundunar yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane dauke da wayar salular wani dan majalisar Tarayya

Rundunar yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane dauke da wayar salular wani dan majalisar Tarayya

Ya ce sun samu nasarar yin kamen ne a ranar 18 ga watan nan, yayin da suka je bayarda agajin gaggawa a wani gurin da aka yi hatsarin mota a yankin Musawa.

Ya ce sun tsargu a lokacin da suka ga ciwon harbin bindiga a jikin daya daga cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su bayan da suka kai su asibiti.

A don haka ne jami’an ‘yan sandan suka bazama kauyukan da ke da makwabtaka da gurin da aka yi hatsari suka yi ta tambaya ko akwai inda aka yi fashi da makami.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel