Ka ji abin da Saraki ya fada bayan Gwamnati ta daukaka karar sa

Ka ji abin da Saraki ya fada bayan Gwamnati ta daukaka karar sa

– Shugaban Majalisar Dattawa Saraki yayi magana game da shari’ar sa

– Bukola Saraki yace bai damu ba don a daukaka karar ba

– Shugaban Majalisar ya nanata cewa bai yi wani ba daidai ba

Gwamnatin Tarayya ta daukaka karar Bukola Saraki. Kotu ta wanke Saraki daga duk laifin da ake zargin sa. Shugaban Majalisar yace don a daukaka kara ba komai bane.

Ka ji abin da Saraki ya fada bayan Gwamnati ta daukaka karar sa

CCT: Bukola Saraki ya dura kan Gwamnati

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yace don Gwamnatin ta daukaka karar sa ba komai bane. Saraki yace tabbas shi fa yana da gaskiya don haka Kotu ta wanke sa daga duk laifuffukan da ke kan san har 18.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta tasa Tsohuwar Minista Diezani a gaba

Ka ji abin da Saraki ya fada bayan Gwamnati ta daukaka karar sa

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Alkali Danladi

Yusuf Olaniyonu da ke magana da bakin Shugaban Majalisar yace don a daukaka kara ba abin da zai canza don kuwa yana da gaskiya saboda haka Kotu ba za ta canza shari’ar da tayi ba. Saraki ya zargi wasu cikin Gwamnati da kokarin ganin bayan sa.

Kun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya leka Kasa mai-tsarki Saudiya domin ibadar Umrah. Dama dai Majalisa ta tafi hutun Sallah yayin da ake shirin kare azumi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Nnamdi Kanu ya tara cincirandon Jama'a

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel