Rikita-Rikita: Sanata Abu Ibrahim ya maka wani tsohon dan majalisa kotu bisa zargin cin zarafi

Rikita-Rikita: Sanata Abu Ibrahim ya maka wani tsohon dan majalisa kotu bisa zargin cin zarafi

Sanata Abu Ibrahim wanda mutanen mazabarsa a jihar Katsina suka yi masa ruwan duwatsu a wata ziyara da ya kai mazabar tasa ya maka wani tsohon dan majalisa Sani Liti 'Yankwani a kotu akan zargin bata masa suna a idonuwar mutanen mazabarsa.

Sanata Abu Ibrahim ya zargi tsohon dan majalisar jihar da mai da shi makaryaci wanda hakan zai iya rusa masa hanyar cin abincinsa a harkokin siyasa sannan kuma hakan na iya tunzura mutanen mazabarsa su ci masa mutunci.

Ibrahim ya nuna shaidunsa da ya samo daga jaridu hudu a kotu wanda ya nuna irin maganganun da Sani Liti 'Yankwani ya ke yi akan sa wanda hakan yana ci masa tuwo a kwarya.

NAIJ.com ta samu labarin cewa kotun dake sauraren karar ta daga shari’ar zuwa 3 ga watan Oktoba domin a lokacin ne lawyan da ke kare Abu Ibrahim wato Hauwa Wada za ta samarwa kotu takardun zargin da suke da shi akan Liti 'Yankwani.

Rikita-Rikita: Sanata Abu Ibrahim ya maka wani tsohon dan majalisa kotu bisa zargin cin zarafi

Rikita-Rikita: Sanata Abu Ibrahim ya maka wani tsohon dan majalisa kotu bisa zargin cin zarafi

Bayan haka Hauwa Wada ta amince Alkali Maikata Bako ya daga shari’an zuwa 3 gawatan Oktoba bayan lauyan dake kare Liti 'Yankwani Alex Ajode ya roko alfarman kotun ta yi hakan shima.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a kotun Liti 'Yankwani ya ce kotun Shari’a da ke sauaraen karan da Abu Ibrahim ya shigar akansa bata da hurumin sauraren irin wannan kara, inda yace yin haka sabawa dokar kasa ne.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel