Osinbajo ya kira taron gaggawa kan rikicin kabilancin Mambila a jihar Taraba

Osinbajo ya kira taron gaggawa kan rikicin kabilancin Mambila a jihar Taraba

- Osinbajo ya gana da shugabannin hukumomin tsaro tare da gwamnan jihar Taraba kan rikicin yankin Mambila a jihar

- Osinbajo ya mika ta’aziyyar a madadin gwamnatin tarayya ga iyalan wadanda rikicin ta rutsa da su

- Sakataren kungiyar kare fulanin ya zargi hukumomin yankin da hana bada agaji ga fulanin da rikicin ta shafa

Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya kira wata taron gaggawa inda kuma ya kafa wani kwamitin bincike kan rikicin yankin Mambila a jihar Taraba.

Farfessa Osinbajo, ya kuma mika ta’aziyyar a madadin gwamnatin tarayya ga iyalan wadanda suka rasha ‘yan uwarsu a wannan rikicin.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, babban maitaimakin na musammam kan harkokin yada labarai ga mukaddashin shugaban kasa, Hamisu Ibrahim ya bayyana hakan bayan wani zaman da aka yi a kan batun rikicin kabilancin yankin Mambila da ke jihar Taraba.

Osinbajo ya kira taron gaggawa kan rikicin kabilancin Mambila a jihar Taraba

Rikicin kabilancin yankin Mambila da ke jihar Taraba

Ibrahim ya ci gaba da cewar Farfessa Osibanjo ya gana ne da shugabannin hukumomin tsaro tare da gwamnan jihar Taraba Darius Isiyaku ta yadda za a kawo karshen rikicin da kuma gano bakin zare.

Yawa-yawan tashe tashen hankula da ake samu musamma yankunan arewacin kasar nada nasaba da rashin hukunta wadanda suke tada wadannan fitintinun, shi yasa ake ci gaba da fuskantar ire-iren wadannan rigingimun. Kamar yadda ake gani a jihohin kaduna, da Flato, da Nasarawa, da Benue da kuma Taraba.

KU KARANTA: Kotu ta umarci gwamnatin jihar Legas ta biya diyyar rusa gidajen mazauna gaban teku

A nasa bayani, sakataren kungiyar kare fulanin wato Pastoral Resolve Dakta Sale Momale ya zargi hukumomin yankin da hana bada agaji ga fulanin da rikicin ya rutsa da su, tare kuma da toshe kafofin isar da taimako a cikin yankin.

Tuni ita kuma gwamnatin jihar ta Taraba ta yi watsi da wannan tuhumar da kungiyar ta yi mata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikicin kabilanci tsakanin Yarabawa da Hausawa mazaunan garin Ile-Ife da ke jihar Osun

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel