Daga jihar Legas aka umurci kabilar Igbo su fice daga arewa – Inji wani babban lauya

Daga jihar Legas aka umurci kabilar Igbo su fice daga arewa – Inji wani babban lauya

- Femi Falana ya ce daya daga shugabanin kungiyoyin matasan arewa da suka umurci ‘yan kabilar Igbo ficewa daga arewa mazauna a Legas ne ba arewa ba

- Falana ya ce dole ne a sake fasalin al'amuran kasar idan ana so a warware matsalolin da kasar ke fuskanta yanzu

- Falana ya yi Allah wadai da kalaman kakakin Kungiyar Dattawan Arewa Foru, Farfesa Ango Abdullahi na goyon bayan shugabanin kungiyoyin matasan arewa

Babban lauyan nan mai kare hakkin bil adama da tsarin mulkin kasa, Femi Falana (SAN) ya ce a ranar Alhamis, 22 ga watan Yuni cewa daya daga cikin shugabanin kungiyoyin matasan arewacin kasar da ya bayar da watanni uku ‘yan kabilar Igbo su fice daga yankin arewa ba ya zama a arewa, mazauna a Legas ne.

Falana ya ce sake fasalin al'amuran a kasar dole ne a warware ta yanzu domin kasar ta ci gaba. Babban lauyan ya yi wannan magana ne a wani taron manema labarai wanda kungiyar kwadago ta shirya a birnin Abuja.

KU KARANTA: Bai kamata Kwankwaso ya ce kada a kama matasan Arewa ba - Inji Balarabe Musa

Daga jihar Legas aka umurci kabilar Igbo su fice daga arewa – Inji wani babban lauya

Lauya mai kare hakkin bil adama da tsarin mulkin kasa, Femi Falana (SAN)

Falana ya ci gaba da cewa mutumin da ya sanar da cewa duk ‘yan kabilar Igbo su fice daga yankunan arewa ba ya zama a arewa; ya na zaune ne a Legas. Ina tabbatar makui da cewa Shettima Yerima yana zaune a Legas. Saboda haka ka kasance a Legas kuma kana bada umurnin cewa wasu ‘yan kasa su fice daga yankunan ku ba dai-dai ba ne kuma ba shine zai warware rikicin da ke kasa ba.

NAIJ.com ta ruwaito cewa Falana ya yi Allah wadai da kalaman kakakin Kungiyar Dattawan Arewa Foru, Farfesa Ango Abdullahi, inda yake goyon bayan wa’adin da shugabanin kungiyoyin matasan arewa suka wa Igbo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta tattauna da shugaban 'yan fafutukar kafa yankin Biyafara, Nnamdi Kanu a cikin wannan bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel