Bikin Sallah: Manyan jaruman Kannywood za su ketara Najeriya domin gudanar da wasanni

Bikin Sallah: Manyan jaruman Kannywood za su ketara Najeriya domin gudanar da wasanni

- Manyan jaruman Kannywood za su tafi kasar waje don shagulgulan sallah karama

- Adam A. Zango ya shirya tsaf domin tafiya jamhuriyar Nijer inda zai kayatar da masoyansa da ke can a lokacin bikin Sallah

- Kasar Ghana kuwa za ta samu bakuncin Jamila Nagudu, Halima Atete da Zaharadeen Sani.

Wasu manyan jaruman kamfanin shirya fina-finan Hausa na Kannywood ba za su yi shagulgulan bikin karamar Sallah a gida Najeriya ba, inda suka shirya yin wasanni a kasashe masu makwabtaka da kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa Adam A. Zango ya shirya tsaf domin tafiya jamhuriyar Nijer inda zai kayatar da masoyansa da ke can a lokacin bikin Sallah.

KU KARANTA KUMA: Kamfanin Kannywood ta shirya sakin manyan fina-finai guda 7 da karamar Sallah

Bikin Sallah: Manyan jaruman Kannywood za su ketara Najeriya domin gudanar da wasanni

Bikin Sallah: Manyan jaruman Kannywood za su ketara Najeriya domin gudanar da wasanni

A daya bangaren kuwa kasar Ghana kuwa za ta samu bakuncin Jamila Nagudu, Halima Atete da Zaharadeen Sani.

Zaharaddeen ya bayyana cewa za su amsa gayyata ne daga dumbin masoyansu da ke can, wadanda suka bukaci su zo su nishadantar da su a lokacin bikin sallar.

Ya kara da cewa mutanen Ghana su na matukar kaunar shirye shiryen Kannywood kuma wannan ita ce damar su nuna masu cewa suna tare da su.

Za su bar Najeriya a yau Juma’a, kuma kowannen su zai yi wasanni a gurare daban daban.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com TV: Tsakanin maza da mata wa ya fi karya?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel