Bai kamata Kwankwaso ya ce kada a kama matasan Arewa ba - Inji Balarabe Musa

Bai kamata Kwankwaso ya ce kada a kama matasan Arewa ba - Inji Balarabe Musa

- Balarabe Musa ya ce bai kamata Kwankwaso ya ce kada a kama matasan Arewa ba

- Ya ce akwai bukatar a kama matasan da sukayi wannan kalami na baiwa 'yan Igbo wa'adin barin gari

- Kungiyoyin Yarbawa ta Afeniferi da ta kabilar Ibo Ohanaeze, su ma sun kalubalanci Sanata Kwankwaso kan kin amincewa da kama matasan da ya yi

Balarabe Musa ya ce bai kamata Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce kada a kama matasan Arewa da suka baiwa kabilar Igbo wa'adin barin yankin Arewa ba.

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya kuma kara da cewa ya kamata a kama matasan da suka yi wannan furucin.

Bai kamata Kwankwaso ya ce kada a kama matasan Arewa ba - Inji Balarabe Musa

Balarabe Musa ya kalubalanci Rabi'u Musa Kwankwaso

A gefe daya kuma, kungiyoyin Yarbawa ta Afeniferi da ta kabilar Ibo Ohanaeze, su ma sun kalubalanci Sanata Kwankwaso kan kin amincewa da kama matasan da ya yi.

KU KARANTA KUMA: An kai karar sarauniyar Ingila ga 'yansanda

A baya NAIJ.com ta tattaro cewa tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce kama matasan arewa da wasu gwamnonin arewacin kasar nan ke shirin yi don sun baiwa kabilar Igbo wa'adin barin yankin arewa ba daidai bane, maimakon haka ya kamata gwamnonin su yi zama da kungiyoyin matasan domin fahimtar juna.

A yayin da ya ke magana kan shugaba Buhari kuma a yayin hirarsa da 'yan jaridu, sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kara da cewa "Idan har shugaba Buhari zai sake tsayawa takara a 2019 babu damuwa, saboda idan mutum yana jinya a asibiti, ba wai hakan na nufin na waje yafi shi lafiya bane.

Wannan hukunci ne na Ubangiji kuma babu wanda zai kalubalance shi". Kwankwaso ya kuma karyata batun cewa zai canja jam'iyya, inda ya ce yana nan a jam'iyyar APC domin tana yi masa adalci. Sanatan ya kara da cewa har yanzu yana da masoya a Kano da yankin Arewa fiye da yadda ake zato.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel