Yansandan jihar Kano sun kama ɓarayin babura su 17

Yansandan jihar Kano sun kama ɓarayin babura su 17

Hukumar Yansandan jihar Kano tace ta kama mutane 17 da take zargi da satar babura da adaidaita sahu a kwaryar birnin Kano. Inji rahoton Daily Trust.

Kaakakin rundunar, DSP Musa Majia ne ya bayyana haka yayin dayake gabatar da barayin ga manema labaru a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni.

KU KARANTA: Yansanda sun yi wawan kamu: Sun kama zauna gari banza su 120 a jihar Sakkwato

Majia yace sun samu nasarar kama barayin ne bayan kaddamar da wani aiki na musamman mai taken “Operation shege ka fasa” domin magance yawan satar babura da adaidaita sahu a jihar Kano.

Yansandan jihar Kano sun kama ɓarayin babura su 17

Yansanda

“Biyo bayan haka mun kama barayin babura da dama a unguwannin Unguwa Uku, Hotoro, Hausawa, Zoo road, Gyadi Gyadi da Bello road, cikin wadanda muka kama har da barawon daya saci sama da babura 100 a makarantu, masallatai da asibitoci.” Inji shi.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Kaakakin yana fadin wasu daga wandanda aka kama suna yima direbobin a daidaita sahu fashi da makami.

Daga karshe yace kwamishinan yansandan jihar, Rabiu Yusuf ya umarci dukkanin kwamandojin rundunar dasu dage wajen ganin an cigaba da kama barayin babura a Kano, har ma das auran bata gari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shirin yi ma Sanata kiranye

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel