Yan Shi’a zasu yi gangamin tattakin tunawa da ranar Qudus a yau Juma’a

Yan Shi’a zasu yi gangamin tattakin tunawa da ranar Qudus a yau Juma’a

- A yau ne yan shi'a zasu gudanar da tattakin ranar Qudus

- Haryanzu malamin yan shi'a Zakzaky na can daure

Kungiyar mabiya addinin Shi’a ta shirya gabatar da gagarumin gangamin tunawa da ranar Qudus a ranar Juma’a 23 ga watan Yuni a duk fadin jihohi 24 na Najeriya.

Kaakakin kungiyar, Ibrahim Musa yayi kira ga dukkanin jama’a dasu shigo cikinsu don yin wannan gangami domin su nuna rashin amincewarsu da cin zarafin da ake yi ma Falasdinawa.

KU KARANTA: Sarkin Saudiyya yayi kakkaɓa, tankaɗe da rairaya

Sai dai a bayan wannan tattaki nasu ya kan janyo rikici tsakaninsu da jami’an tsaro.

Sanarwar tace “Zamu gabatar da tattakin ne domin mika korafin mu kan kaka gida da Yahudawa suka yi a kasar Palestine. A yanzu haka Yahudawan share wuri zauna sun kwace babban masallaci na uku a musulunci, Masallacin Aqsa, don haka ne zamu nuna rashin amincewar da yadda ake cutar da Falasdinawa….”

Yan Shi’a zasu yi gangamin tattakin tunawa da ranar Qudus a yau Juma’a

Yan Shi’a

NAIJ.com ta ruwaito Kaakakin na nanata bukatar kungiyar da gwamnati ta sako musu shugabansu, Ibrahim El-Zakzaky, inda yace “Yau kwanakinsa 588 duk da umarnin da kotu ta bayar da a sake shi.”

Yan Shi’a zasu yi gangamin tattakin tunawa da ranar Qudus a yau Juma’a

Yan Shi’a

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Najeriya giwar Afirka

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel