An daina zaɓe a yankin kudu maso gabas, har sai an bamu ƙasar Biyafara –Inji Nnamdi Kanu

An daina zaɓe a yankin kudu maso gabas, har sai an bamu ƙasar Biyafara –Inji Nnamdi Kanu

- Shugaban kungiyar IPOB yace ba zasu bari a yi zabe a kasar Biyafara ba

- Kanu ya bayyna ma magoya bayansa hakan a bidiyo

Shugaban kungiyar rajin samar da kasar Biyafara, Nnamdi Kanu ya gargadi wgamnati da cewa jama’an yankin kabilar ibo ba zasu kara yin wani zabe ba har sai an basu kasar Biyafara.

Kanu ya bayyana haka ne yayin da wasu gungun magoya bayansa suka kai mai ziyara a gidansa inda yace zasu fara kaddamar da wannan kudiri nasu a jihar Anambra, ind ayace ba zasu bari a gudanar da zaben gwamnan jihar ba.

KU KARANTA: Atiku ya fara shirin fafatawa da Sule Lamido a takarar shugaban ƙasa 2019

Wannan batu na Kanu ya watsu ne ta wani bidiyo dake yawo a kafafen sadarwa, sai dai ba’a tantance yaushe ne aka dauki wanna bidiyo ba, sakamakon hakan na cikin sharuddan ada mai shari’a Binta Nyako ta gindaya masa kafin ta bashi beli, kada ya tara jama’a a gangami.

An daina zaɓe a yankin kudu maso gabas, har sai an bamu ƙasar Biyafara –Inji Nnamdi Kanu

Nnamdi Kanu

“A shekarar 2019, ba zamu bari jama’an mu su yi zaben shugaban kasa, ko na Sanata, ko na majalisar tarayya, ko na majalisar dokokin jiha, har ma dana kansila ba, muddin gwamnati bata bamu kasra Biyafar ba,” Inji Kanu

A wani hannun kuma, Kanu ya shaida ma gidan talabijin an Al-Jazeera cewa bai damu da duk matsalar da zai iya fuskanta ba a gaban kotun data bada belinsa dangane da furucin dayake yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo muku yadda aka saki Kanu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel