Alkalin kotun Najeriya ta ɗaure Ba’amurke kan laifin zambatar ýan Najeriya 3

Alkalin kotun Najeriya ta ɗaure Ba’amurke kan laifin zambatar ýan Najeriya 3

Wata kotun garin Legas ta aika da wani dan kasar Amurka mai suna Marco Ramirez zuwa kurkukun kirikiri don a sakaya mata shi sakamakon damfarar wani dan Najeriya da yayi kudi har dala 650,000.

Shi dai wannan ba’amurken ya damfari dan Najeriyan ne da sunan zai sama masa katin zaman dan kasa a Amurka, sai dai ya musanta zargin da hukumar EFCC ke tuhumarsa da shi a gaban kotun.

KU KARANTA: Maharan Boko Haram sun kai harin ƙunar baƙin wake kasar Kamaru

Lauya mai shihgar da kara V.O Aigboje bayyana ma kotu cewa Marco ya aikata laifukan da ake zarginsa dasu ne a shekarar 2013 daga watan Feburairu zuwa watan Agusta.

Alkalin kotun Najeriya ta ɗaure Ba’amurke kan laifin zambatar ýan Najeriya 3

Ba’amurke Marco

Laifukan sun hada da damfarar Mista Godson Echejue dala 545,00 da sunan zuba hannun jari a kamfaninsa domin sama masa katin shaidar zama dan kasar Amurka. Haka zilak majiyar NAIJ.com ta ruwaito lauyan na tuhumar Marco da damfarar Abubakar Umar dala 10,000 da sunan yin kasuwanci a Amurka.

Har ila yau, EFCC na karar Marco akan damfarar Olukayode Sodimu dala 10,000, kan haka ne lauyan EFCC ya bukaci a garkame Marco a Kurkuku inda yace hukumar bata da gadon da zata bashi a ofishinta.

Sai dai lauyan Marco ya nuna tirjiya da wannan bukata ta lauyan EFCC, ind aya bukaci Marco ya cigaba da zama a EFCC har sai ya samu beli, amma alkali Josephine Oyefeso tace ta ki wayon, inda ta bada umarin a sakaya mata Marco a kurkkukun Kirikiri.

Daga nan sai mai shari’a Josephine ta dage sauraron karar har zuwa ranar 3 ga watan Yuli, kamar yadda kamfanin dillancin labaru ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yakin Sojoji da Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel