Allah ya haska zuciyar wasu mata a watan Azumin Ramadana (Hotuna)

Allah ya haska zuciyar wasu mata a watan Azumin Ramadana (Hotuna)

- Wasu yan mata biyu sun shiga addinin Islama a jihar Sakkwato

- Yan matan sun musulunta ne a Masallacin unguwar Koko

Wata shafin sadrawa daga cikin shafukan dandalin sadarwa na Facebook, Rraiya ta ruwaito musulunci ya samu karuwa da wasu yan mata da suka gane gaskiya a ranar Alhamis 27 ga watan Ramadana a jihar Sakkwato.

Yan matan, inji majiyar NAIJ.com sun amshi musulunci ne ta hannun wani shahararren malami dake gabatar da Tafsirin Al-Qur’ani mai girma, Mal Bashar Ahmad Sani a wani masallaci dake unguwar Koko ta jihar.

KU KARANTA: Hattara: Ana yi ma Fulani kisan kiyashi a jihar Taraba (HOTUNA)

Musuluntar matan ke da wuya, sai suka sauya sunayensu zuwa Fatima da Jamila, kamar yadda addinin ya basu dama.

Allah ya haska zuciyar wasu mata a watan Azumin Ramadana (Hotuna)

Yan matan tare da malamin

Alkalummma sun nuna cewar an samu karuwar mutane da dama da suka shiga addinin musulunci a wannan watan Ramadana, wata mai albarka na bana, Allah ya kara shiryar damu hanya madaidaciya, amin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon wani direban Fasto daya musulunta

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel