Ta tabbata: INEC ta sanar da Dino Melaye cewa kwanakin shi sun kusa karewa

Ta tabbata: INEC ta sanar da Dino Melaye cewa kwanakin shi sun kusa karewa

– Hukumar zabe ta tabbatar wa Sanata Melaye cewa magana tayi karfi

– Yanzu haka dai maganar koro Sanatan na Jihar Kogi ta kankama

– Dino Melaye yace Jama’a za su leka gidan yari a dalilin hakan

INEC ta aikawa Sanata Dino Melaye takarda cewa ya shirya. Hukumar tace ta samu korafi daga Jama’a su na shirin maido sa gida. Sanata Dino Melaye na cikin tsaka mai wuya a halin yanzu.

Ta tabbata: INEC ta sanar da Dino Melaye cewa kwanakin shi sun kusa karewa

Sanata Melaye zai bar Majalisa ba girma ba arziki

Ku na sane cewa Mutanen mazabar Yammacin Jihar Kogi na shirin yi wa Sanatan su Dino Melaye kiranye wanda yanzu abu ya kai inda ya kai. Hukumar zabe dai ta tabbatar da wannan magana inda tace tuni har ta sanar da Sanatan.

KU KARANTA: Shirin kiranye: Dino Melaye yayi magana

Ta tabbata: INEC ta sanar da Dino Melaye cewa kwanakin shi sun kusa karewa

INEC ta sanar da Sanata Melaye

Kwamishinan zabe na Arewa maso tsakiya Mohammed Haruna ya bada wannan jawabi a takarda. Jim kadan dai za a fara shirin kada kuri’ar raba gardama da zarar an tantance sa-hannun mutanen mazabar a Ranar 3 ga watan gobe.

Dama kun dai ji cewa mutane 188,588 su ka sa hannu inda su ka nemi a maido Sanata Dino Melaye gida daga Majalisar Dattawa inda yake wakiltar mazabar sa ta Yammacin Kogi. Doka dai ta bada dama a fatattako ‘Dan Majalisa idan akasarin Jama’a ba su son wakilcin sa.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sababbin Jam'iyyu za su kawo mafita a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel