Ya kamata gwamnonin arewa su yi zama da kungiyoyin matasan arewa domin fahimtar juna – Inji Kwankwaso

Ya kamata gwamnonin arewa su yi zama da kungiyoyin matasan arewa domin fahimtar juna – Inji Kwankwaso

- Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya shawarci gwmanonin arewacin kasar cewa ya kamata su tattauna da shugabanin kungiyoyin matasan arewa

- Sanatan ya ce idan har shugaba Buhari yace zai sake tsaya takara a 2019 ba abun damuwa bane

- Kwankwaso ya ci gaba da cewa yankunan da kabilar Igbo suka mamaye a yankunan arewa, ya fi girman yankinsu baki daya

Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce kama matasan arewa da wasu gwamnonin arewacin kasar nan ke shirin yi don sun baiwa kabilar Igbo wa'adin barin yankin arewa ba daidai bane, maimakon haka ya kamata gwamnonin su yi zama da kungiyoyin matasan domin fahimtar juna.

A yayin da ya ke magana kan shugaba Buhari kuma a yayin hirarsa da 'yan jaridu, sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kara da cewa "Idan har shugaba Buhari zai sake tsayawa takara a 2019 babu damuwa, saboda idan mutum yana jinya a asibiti, ba wai hakan na nufin na waje yafi shi lafiya bane. Wannan hukunci ne na Ubangiji kuma babu wanda zai kalubalance shi".

Kwankwaso ya kuma karyata batun cewa zai canja jam'iyya, inda ya ce yana nan a jam'iyyar APC domin tana yi masa adalci. Sanatan ya kara da cewa har yanzu yana da masoya a Kano da yankin Arewa fiye da yadda ake zato.

KU KARANTA: Sanata Kwankwaso yayi magana game da lafiyar Buhari da 2019

Ya kamata gwamnonin arewa su yi zama da kungiyoyin matasan arewa domin fahimtar juna – Inji Kwankwaso

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, a yayin da yake tofa albarkacin bakinsa ga wa’adin watan uku da wasu shuwagabanin matasan arewacin kasar suka ba ‘yan kabilar Igbo, sanata Kwankwaso yace yankunan da kabilar Igbo suka mamaye a yankunan arewa, ya fi girman yankinsu baki daya dake Kudu maso gabashin kasar, kuma ba karamin arziki suka tara a arewa ba, don haka ba zasu iya barin arewa ba, a cewar Kwankwaso.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Cikakken bayanin mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo kan yakin basasan Najeriya a cikin wannan bidiyon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel