Kotu ta umarci gwamnatin jihar Legas ta biya diyyar rusa gidajen mazauna gaban teku

Kotu ta umarci gwamnatin jihar Legas ta biya diyyar rusa gidajen mazauna gaban teku

- Kotu ta bukaci gwamnatin jihar Legas da ta dakatar da aikin rusa gidajen jama’ar da ke rayuwa a gabar ruwan teku

- Gwamnatin ta ce tana yin aikin ne saboda rage yawan masu aikata laifufuka

A cikin watan Oktoban da ya gabata ne mazauna unguwannin dake gabar teku a jihar Legas sun shigar da kara gaban kotu bayan da gwamnatin jihar Legas ta rusa masu gidaje kwana.

Kotun ta umurci gwamnatin jihar Legas da ta dakatar da aikin rusa gidajen jama’ar da ke rayuwa a gabar ruwan teku, aikin da gwamnatin ta ce tana yin sa ne domin rage yawan masu aikata laifufuka.

Kotu ta umarci gwamnatin jihar Legas ta biya diyyar rusa gidajen mazauna gaban teku

Kotu ta umarci gwamnatin jihar Legas ta biya diyyar rusa gidajen mazauna gaban teku

Hukuncin kotun ya bukaci gwamnati ta shiga tattaunawa da jama’a kan yadda za a biya su kudaden diyya ko kuma ta samar masu inda zasu zauna.

Wata Khadija Yusuf dake rayuwa a irin wadannan unguwanni, ta ce sun yi farin ciki da hukuncin na kotun, ta ce rusa matsuguninsu da suke rayuwa a Legas ya tursasawa mutane da dama barin garin duk da sun shafe shekaru suna rayuwa domin samun na abinci a unguwanni.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel