Mutane da yawa za su tafi kurkuku saboda kiranyen da aka yi min – Dino Malaye

Mutane da yawa za su tafi kurkuku saboda kiranyen da aka yi min – Dino Malaye

- Dino Malaye ya ce ya yi alkawarin cewa duk wadanda ke da hannu a kiranyen da aka yi ma shi za su kare ne a kurkuku

- Ya ce ya yi alkawarin cewa duk wadanda ke da hannu a kiranyen da aka yi ma shi za su kare ne a kurkuku

Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Malaye ya ce ya yi alkawarin cewa duk wadanda ke da hannu a kiranyen da aka yi ma shi za su kare ne a kurkuku.

A wata hira da gidan talabijin na Channels ta yi da shi, Malaye ya kira yunkurin yi masa kiranyen a matsayin abun dariya wanda ba zai kai ko ina ba.

A cewar shi “Babu wanda zai dauki wannan lamari da muhimmanci saboda siyasar kudi ce kawai.

“Mun gano cewa akwai sunayen matattun mutane a cikin wadanda suka sanya hannu, haka kuma akwai sa hannu da yawa da aka yi da rubutu iri daya. Ha’inci ne da bai yi tasiri ba."

Mutane da yawa za su tafi kurkuku saboda kiranyen da aka yi min – Dino Malaye

Mutane da yawa za su tafi kurkuku saboda kiranyen da aka yi min – Dino Malaye

A don haka ne Malaye ya ce “Na yi alkawari mutane da yawa za su tafi kurkuku akan wannan al’amari.”

A jiya Laraba ne dai aka mika wa hukumar zabe ta kasa INEC sa hannun mutane 188580 da ke bukatar sanatan ya dawo gida.

Wannan adadi ya kunshi kaso 52.3 na ‘yan mazabar Malaye.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel