Abin da ya sa Inyamurai ba za su iya barin Arewa ba – Kwankwaso

Abin da ya sa Inyamurai ba za su iya barin Arewa ba – Kwankwaso

– Sanata Kwankwaso yace Inyamurai ba su isa su bar Kasar nan ba

– Kwankwaso yace Inyamuran sun yi nisa wajen kasuwanci a Arewa

– Tsohon Gwamnan dai yace son rai ya jawo wannan yunkuri

Tsohon Gwamna Injiniya Kwankwaso yayi magana game da Biyafara. Kwankwaso yace son rai ya sa wasu ke kiran a raba Najeriya. A cewar sa ba mamaki jagoran tafiyar Nnamdi Kanu na neman kujera ne.

Abin da ya sa Inyamurai ba za su iya barin Arewa ba – Kwankwaso

Kwankwaso ya bayyana dalilin da ya sa ake kira a raba Najeriya

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso yace Inyamurai ba su isa su bar Arewa ba don kuwa Yankin ya zama masu fiye da gida. A cewar Sanatan kasuwancin da Inyamuran ke yi a Arewacin kasar ya fi karfin a tafi a bari.

KU KARANTA: Kul El-Rufai ya kama Matasan Arewa Inji Kwankwaso

Abin da ya sa Inyamurai ba za su iya barin Arewa ba – Kwankwaso

Ko takara Nnamdi Kanu yake shirin tsayawa ne a zabe mai zuwa?

Kwankwaso ya kara da cewa Mutanen kasar Ibo da ke Arewa su na matukar jin dadin yankin wanda asali ma irin walawar da su ka samu a nan ba za ta zama daya da ta Kasar su ba. Kwankwaso yace ba mamaki Nnamdi Kanu na shirin tsayawa takara ne a zabe mai zuwa.

Rabi’u Musa Kwankwaso Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanata a yanzu ya ba Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai shawarar matakin da ya kamata ya bi wajen kawo karshen rikicin da ke nema ya barke tsakanin Inyamurai da ‘Yan Arewa.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Me ya dace ayi da Evans ?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel