Majalisa za ta kafa dokar rage tsadar kudin haya a Najeriya

Majalisa za ta kafa dokar rage tsadar kudin haya a Najeriya

- Majalisar dattawan Najeriya ta fara aiki akan wani kudiri da ke da nufin rage tsadar kudaden hayar da ake biya a fadin kasar

- Sanata Dino Malaye ne ya bayyana haka kamar yadda wata sanarwa daga ma’aikatar gidaje da ayyuka ta bayyana

Rahotanni sun kawo cewa majalisar dattawan Najeriya ta fara aiki akan wani kudiri da ke da nufin rage tsadar kudaden hayar da ake biya a fadin kasar Najeriya.

Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma kuma shugaban kwamitin majalisa akan babban birnin tarayya Sanata Dino Malaye shi ya bayyana haka kamar yadda wata sanarwa daga ma’aikatar gidaje da ayyuka ta bayyana.

Majalisa za ta kafa dokar rage tsadar kudin haya a Najeriya

Majalisa za ta kafa dokar rage tsadar kudin haya a Najeriya

Sanarwar wacce ta fito a jiya Laraba, 21 ga watan Yuni a Abuja na dauke da sa hannun daraktan yada labarai na ma’aikatar, Eno Olotu.

A sanarwar, Malaye ya bayyana yadda Kudirin mai suna ‘Rent Edit Bill’ zai bayarda kariya ga ‘yan haya da masu bada hayar, kuma ya taimaka wajen rage tsadar kudaden hayan a Abuja da kasar baki daya.

Ya ce za a kammala aiki akan kudiri kafin zuwa karshen majalisa ta 8.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel