Batutuwan da majalisar ministoci ta amince da su a wannan mako

Batutuwan da majalisar ministoci ta amince da su a wannan mako

- Majalisa ta yi na'am da gudanar da taron karawa juna sani kan halin da harkar ilimi ya riski kansa a ciki

- Ministan ilimi ya ce majalisar ministoci ta yi watsi da shawarwarin da ma'aikatar ilimi ta gabatar

A zaman da majalisar ministoci ta yi a wannan mako a karkashin jagorancin Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ta amincewa da gudanar da taron karawa juna sani kan rikicin da harkar ilimi a kasar nan ya tsinci kansa a ciki a yau.

Da yake karin haske game da zaman majalisar, Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya ce majalisar ministocin ta yi watsi da shawarwarin da ma'aikatar ilimi ta gabatar game da mafita kan rikicin a maimakon haka majalisar ta nemi a gudanar da taron a cikin makonni biyu.

Batutuwan da majalisar ministoci ta amince da su a wannan mako

Batutuwan da majalisar ministoci ta amince da su a wannan mako

Haka kuma Ministan ya musanta rahotannin da ake yayatawa kan cewa an soke koyar da darasin addini Kirista a makarantun gwamnati inda ya bayyana masu yayata wannan jita- jitar a matsayin masu neman janyo rudani a cikin kasa wanda a kan haka ya gargade su ka su daina.

A baya NAIJ.com ta tattaro cewa mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman majalisa a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni, a bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda a yanzu yake jinya a birnin Landan.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel