Hukumar Kwastan ta yi gargadi kan yaduwar gurbataccen shinkafa

Hukumar Kwastan ta yi gargadi kan yaduwar gurbataccen shinkafa

- Hukumar Kwatam ta gargadi alúmman Najeriya kan yaduwar gurbataccen shinkafa

- Ta sanar da cewa shinkafar ta cika kasuwanni a fadin kasar

- An umurci jama'a da su rungumi shinkafa 'yar gida

Hukumar Kwastan ta Kasa ta yi gargadin cewa a halin yanzu gurbatacciyar shinkafa wadda ake shigowa da ita daga Iyakoki ta cika kasuwannin kasar nan.

Shugaban Hukumar na shiyyar Oyo/Osun, Emmanuel Udo-Aka ya ce a kowace rana a shigo da gurbatacciyar shinkafar ta iyakokin kasar nan inda ya nuna cewa cin shinkafar na da matukar lahani ga kiwon lafiya. Ya kuma shawarci al'ummar Najeriya kan su rungumi cin shinkafa wadda ake nomawa a cikin gida.

Hukumar Kwastan ta yi gargadi kan yaduwar gurbataccen shinkafa

Hukumar Kwastan ta yi gargadi kan yaduwar gurbataccen shinkafa

A wani alámari makamancin wannan, NAIJ.com ta rahoto cewa Kamfanin siminti na Dangote dake garin Ibese, na jihar Ogun yace sun kama wata motarsu a garin Ibadan dauke da kayayyakin fasa kauri, kuma suka ta mika shi ga jami’an hukumar hana fasa kauri ta kasa.

Yayin da ake mika direban da yaron motar ga hannun jami’an kwastam din, mataimakin shugaban tsaro na kamfanin, Ali Garba yace sun kama tsohon direban kamfanin Ismaila Abubakar yana tuka motarsu dauke da kaji yankakku, ya nufi jihar Edo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel