Sanata Kwankwaso yayi magana game da lafiyar Buhari da 2019

Sanata Kwankwaso yayi magana game da lafiyar Buhari da 2019

– Sanata Kwankwaso ya tofa albarkacin bakin sa game da zabe mai zuwa

– Sanatan na Jihar Kano yace Allah kadai ya san ko Buhari zai nemi tazarce

– Rabi'u Musa Kwankwaso ya kuma yi magana game da kasafin kudin bana

Sanata Kwankwaso yace su na daidai da Shugaban kasa. Tsohon Gwamnan yace maganar 2019 kuma sai Allah. Sanatan yace dole Majalisa ta duba kasafin kudin kasar da aka aiko ma ta kafin ta amince da shi.

Sanata Kwankwaso yayi magana game da lafiyar Buhari da 2019

Mu ba ‘yan amshin Shatan Gwamnati bane-Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Kwankwaso yace Allah ne zai yi zabi a zabe mai zuwa na 2019. Kwankwaso yace kasancewar Shugaba Buhari na asibiti ba ya nufin sauran ‘Yan siyasar sun fi shi lafiya ko kuma ba zai tsaya takara ba don abu ne na Allah.

KU KARANTA: Kwankwaso ya gargadi Gwamnan Jihar Kaduna

Sanata Kwankwaso yayi magana game da lafiyar Buhari da 2019

Kwankwaso yayi magana game da 2019

Haka kuma Injiniya Rabiu Kwankwaso yace dole Majalisa ta duba kasafin kudin da aka kawo mata kwa-kwaf. Sanatan na tsakiyar Jihar Kano yace Majalisa ta na daidai da Shugaban kasa kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Kun ji cewa Sanata Dino Melaye na Yammacin Jihar Kogi ya shiga uku bayan da Hukumar zabe ta kasa watau INEC ta karbi takardun shaida na cewa mutanen mazabar na Jihar Kogi sun zabi a maido Sanatan da su ka zaba gida.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Nnamdi Kanu ya dage wajen ganin ya ceci Inyamurai

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel