Yansanda sun yi wawan kamu: Sun kama zauna gari banza su 120 a jihar Sakkwato

Yansanda sun yi wawan kamu: Sun kama zauna gari banza su 120 a jihar Sakkwato

- Rundunar Yansandan jihar Sakkwato ta sanya ƙafar wando ɗaya da yan daba

- Kwamishinan yansandan jihar ya bayyana sun kama su da dama

Rundunar Yansandan jihar Sakkwato ta kama yan daba su 120 a fadin jihar bayan ta wani sintiri da fara gabatarwa sati daya data wuce a tsakanin karfe 10 na dare zuwa 4 na asuba.

Kwamishinan yan sandan jihar, Muhammad Abdulkadir ya bayyana haka a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni inda yace inda suka ma mutanen sun hada da unguwar Iraqi, Kwanni da Runjin Sambo.

KU KARANTA: Sarkin Saudiyya yayi kakkaɓa, tankaɗe da rairaya

Daily Trust ta ruwaito kwamishinan yana fadin sun kama matasan da makamai da sua hada da takubba da adduna, kuma tuni suka gurfanar dasu gaban kotu, yayin da suke daure a Kurkuku.

Bugu da kari, kwamishinan ya tabbatar ma al’ummar jihar Sakkwato da cewa rundunarsu nada isassun jami’an tsaro da zasu tabbatar da tsaro a masallatai da sauran wurare a lokacin bukukuwan Sallah.

Daga karshe Kwamishina Abdulkadir ya bukaci jama’an Sakkwato dasu zamto masu bin doka da ka’ida, sa’annan su kawo rahoton duk wani mutumin da basu gamsu da take takensa ga hukumar ta hanyar lambobin wayarsu.

A wani labarin kuma, majiyar NAIJ.com ta ruwaito Kwamishinan yansandan yana bayyana cewar miyagun mutanen da suka yi garkuwa da matashin dan kasuwan nan Alhaji Abubakar Kakirko sun rage kudin fansan da suka nema daga N500,000 zuwa N200,000.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel