Maharan Boko Haram sun kai harin ƙunar baƙin wake kasar Kamaru

Maharan Boko Haram sun kai harin ƙunar baƙin wake kasar Kamaru

- Kimanin mutane takwas ne suka rasa rayukansu a Kamaru

- Mutanen sun mutu ne sakamakon harin kunar bakin wake

Kimanin mutane takwas ne ake sa ran sun riga mu gidan gaskiya biyo bayan wani harin kunar bakin da yan Boko Haram suka kai a garin Kolofata dake Arewacin kasar Kamaru.

Gidan Rediyon Faransa ta ruwaito cikin mutanen da suka mutu har da maharan na Boko Haram, kuma an kai harin ne a babbar kasuwar garin Kolofata lokacin ta cika makil da jama’a suna cinikayya.

KU KARANTA: Babu kuɗi a jam’iyyar APC – Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Ko a farkon watan Yuni sai da aka kai ma garin harin kunar bakin wake, inda sama da mutane 9 suka hallaka, inji majiyar NAIJ.com.

Maharan Boko Haram sun kai harin ƙunar baƙin wake kasar Kamaru

harin ƙunar baƙin wake kasar Kamaru

An danganta yawan samun hare hare a garin Kolofata daga mayakan Boko Haram da kasancewarsa yayi kusa da iyakar Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda Sojoji ke ragargazan Boko Haram.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel