Rabuwan kai: Gwamnonin Najeriya sun gana da Farfesa Yemi Osinbajo

Rabuwan kai: Gwamnonin Najeriya sun gana da Farfesa Yemi Osinbajo

- Mukaddashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya gana da gwamnoni a fadar shugaban kasa jiya Laraba, 21 ga watan Yuni

- Ya tattauna yadda za’a dakile maganganu dake iya tada tarzoma

- Gwamnonin sun yarde cewa zasuyi iyakan kokarinsu wajen tabbatar da cewa Najeriya bata balle ba

Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da gwamnonin jihoho 36 domin tattauna yadda za’a shawo kan maganganun rabuwa da kuma yadda za’a hada kan Najeriya.

Bayan ganawar wacce akayi a fadan shugaban kasa da ke Abuja, gwamnonin sun bayyanwa manema labarai cewa sun yanke shawaran yakan duk wanda zaiyi wani Magana da zai raba kan yan Najeriya.

NAIJ.com ta samu rahoton cewa gwamnaonin sun ce babu abinda irin wadannan maganganu zai tsinana illa Karin talauci, yunwan rashin aikin yi, kuma kowa zai yi hasara idan Najeriya ta rabu.

Rabuwan kai: Gwamnonin Najeriya sun gana da Farfesa Yemi Osinbajo

Rabuwan kai: Gwamnonin Najeriya sun gana da Farfesa Yemi Osinbajo

Game da cewar jaridar Punch, Osinbajo ya bayyana cewa duk dan Najeriyan da ke tunanin cewa Najeriya zata rabu na batawa kansa lokaci ne.

KU KARANTA: Da rabon Dino Melaye yaci taliyar karshe

Yace: “ Ba zamu iya rabuwa ba, kuma duk wanda ke tunanin hakan na batawa kansa lokaci ne kuma ba zamu yarda da hakan ba. Dukkan mu munyi ittifaki."

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel