Badakalar Dabinon Saudiyya: 'A daina bata mana suna' - Kwamishiniya Sadiya Faruk

Badakalar Dabinon Saudiyya: 'A daina bata mana suna' - Kwamishiniya Sadiya Faruk

- Badakalar karkatar da dabinai ta jawo abin kunya

- A Daina Bata Mana Suna Kan Dabinon Saudiyya, Inji Sadiya Farouq

- An baiwa kasar Saudiya Hakuri, kan sace dabinai na sadaka ga masu gudun hijira

Jaridar Rariya ta ruwaito cewa babbar kwamishiniyar Hukamar kula da 'yan gudun hijira ta kasa Hajia Sadiya Umar Farouq, ta yi matukar nuna takaicin ta, tare da alhini akan yadda ake ta kokarin batawa Hukamar da take jagoranta, jihar ta haihuwa (Zamfara), ita kanta dama kasar Nijeriya suna akan wai cewa ta karkatar da dabinon tallafi 'yan gudun hjijra da kasar Saudiya ta baiwa Nijeriya sadaka.

Badakalar Dabinon Saudiyya: 'A daina bata mana suna' - Kwamishiniya Sadiya Faruk

Badakalar Dabinon Saudiyya: 'A daina bata mana suna' - Kwamishiniya Sadiya Faruk

Kwamishiniyar ta bayyyana matukar mamakinta, da takaicinta irin yadda wasu suka yi amfani da kafar sadarwa ta zamani, dama wasu jaridun kasar nan wajen yada labarin kanzon kurege akan cewa ta karkatar da dabinon tallafin zuwa jihar ta haihuwa wato Zamfara.

Kwamishiniyar tace ita dai abunda ta sani shine hukumar ta na iya kokarinta wajen ganin ta kyautatawa 'yan gudun hijira da ma kokarin sauke hakkin da duk ya rataya ga hukumarta.

Kwamishiniyar ta tabbatar da cewa tabbas 'yan gudun hijira da suka fito daga jihar Zamfara su ma suna daga cikin wadanda suka amfana da tallafin dabinon, domin akwai tarin 'yan gudun hijira da rikicin barayin shanu ya rutsa da su kamar sauran sassa na kasar nan.

Haka zalika Sadiya ta kara jaddada cewa hukumarta na iya kokarinta wajen daidaito da raba daidai a duk ayukkan da take yi.

Daga karshe kwamishiniyar ta roki al'umma da su kasance masu bincike da tabbatar da labari kafin yada shi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel