Talakawan Legas sun samu galaba kan gwamnatin jihar

Talakawan Legas sun samu galaba kan gwamnatin jihar

- Babbar kotun jihar Legas ta dakatar da gwamnatin jihar daga ci gaba da rusa gidajen talakawa da ke kusanci da bakin teku

- Yankunan da wannan rusawar ta shafa sun hada da Otodo Gbame da Ikorodu da Otumara da kuma Okun Agban

- Kotun ta bukaci gwamnatin jihar Legas da ta yi karan tsaye ga dokar kasa, musamman ta cin zarafin talakawa

-Kotun ta umarni gwamnatin jihar da ta koma teburin sulhu da mazaunan yankin don kare hakkin talakawan.

Babbar kotun jihar Legas ta dakatar da gwamnatin jihar daga ci gaba da rusa gidajen talakawa ba bisa ka'ida ba tare da umarnin komawa teburin sulhu don kare hakkin talaka.

A zamanta a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni kotun da ke Igboshere ta tabbatar da cewa, gwamnatin jihar Legas ta yi karan tsaye ga dokar kasa, musamman ta cin zarafin talakawa wadanda ta rusawa gidajensu ba tare da basu wa'adi ba.

Misali idan aka duba wadanda ke wuraren da ke kusanci da bakin teku da gwamnati ta lalata tare da haifar da rashin wuraren kwana da ya shafi dubban jama'a. Wurare kamarsu Otodo Gbame da Ikorodu da Otumara da Okun Agban sun fada cikin wannan taskun.

Talakawan Legas sun samu galaba kan gwamnatin jihar

Yankunan da rusawar ta shafa sun hada da Otodo Gbame da Ikorodu da Otumara da kuma Okun Agban

Comrade Mohammed Zanna da ke zama daya daga cikin mazauna wadannan yankuna ya ce akalla mutane 30,000 ke zaune a wurin kuma "idan aka kore su ko aka tada su daga wurin, to ai wani matsugunin za a je a kirkiro a wani wuri." Saboda haka Mohammed Zanna ya goyi bayan da a zauna kan teburin sulhu da mahukuntan jihar ta Legas.

KU KARANTA: El-Rufai ya gaza, ba zai iya mulkin jihar Kaduna ba – Shehu Sani

Wannan matsala dai ta shafi matsuguni sama da 39 duk kuwa talakawa ne da ke zaune a wadannan yankunan.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Barrister Omotayo Enujiga ita ce mai kare hakkin mazauna wannan yanki a gaban kotu da ta bayyana hukuncin kotun da cewa ya yi armashi na komawa teburin sulhu da gwamnati don samun mafita. Su ma mazauna wadannan matsugunan talakawan sun yi farin ciki da hukuncin kotun, sun kuma yi fatan gwamnati za ta mutunta hukuncin kotun.

Gwamnatin jahar Legas ta ce tana daukar matakin rusau ne saboda dalilai na tsaro da kuma kare muhalli.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan matar tace ta rasa yara 4 ga rusa gidajen su da gwamnatin jihar Legas ta yi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel