Boko Haram sun sace mata 16 a harin Damboa

Boko Haram sun sace mata 16 a harin Damboa

- Boko haram sun kai farmaki a tawagar jami'an tsaro kuma sunyi awon gaba da mata 16

- Wanda suka tsira daga wannan farmakin sun bada labarin yadda mayakan boko haram suka bude wa tawagar jami'an tsaro wuta sannan suka tafi da mata guda 16.

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe goma na safiyar Talata a hanyar Damboa lokacin da tawagar jami'an tsaro da ke dauke ya 'yan sanda, motar haya, da kuma magunguna da sojoji da suka taso daga Maiduguri zuwa kudanci Jihar Bornon.

Boko Haram sun sace mata 16 a harin Damboa

Boko Haram sun sace mata 16 a harin Damboa

Ita wannan hanya wanda ta bulle zuwa dajin sambisa ta dade a kulle saboda yawan hari da 'yan boko haram sukeyi a hanyar. An bude hanyar ne a watan satumba na shekara 2016. Kuma bayan bude hanyar, 'yan boko haram din sun cigaba kai ma matafiya farmaki a hanyar.

Komishinan yan sandan Jihar Borno Damian Chukwu ya sanar da manema labarai cewa mutane biyu ne suka rasa rayuwansa a harin. Amma daga baya an kara samun labarin rasuwar mutum daya. komishnan lafiya na Jihar Bornon mai suna Haruna Mshelia yace a cikin manyan motoci guda uku da ke dauke da magunguna, guda daya ne kawai ta isa zuwa inda zata kai kayan, guda biyun sun salwanta a hannun yan boko haram din.

"Wannan abun bakin ciki ne matuka amma dama irin wannan aikin ya gaji haka" inji Mshelia

"An harbi direbar motan ne daga baya wanda ke tare da direban yayi kokarin karbar tukin amma shima aka harbe shi sanadiyar haka motar ta kife"

A cikin wanda suka tsira daga wannan farmakin akwai dan majilisan jiha na Borno da ke wakiltar karamar hukumar Chibok mai suna Aimu Chibok. A hirar tarho da yayi da 'yan jarida, dan majalisan wanda tsohon jami'an yan sanda ne ya koka ga yanda sojoji da yan sanda suka tsara tafiyar tun farko.

Dan majilisan yana tare da mataimakin chairman din karamar hukumar chibok da kuma hakimin garin chibok a lokacin da yan boko haram din suke bude musu wuta. Suna hanyar su ne wajen kadamar da wata aiki na gwamnatin tarayya. Hakimin ya sami rauni a hannu shi kuma mataimakin chairman ya samu rauni a chinya a dalilin harsashin bidiga da ya same su. Duk dai suna asibiti suna karban magani.

"Wannan abin kunya ne kuma ina tunanin cewa yan boko haram din suna da masaniya akan wanan tafiyar tamu" inji dan Majalisan.

"Har illa yau bai dace a cinkushe yan sanda da yawa tare da makamansu ba a cikin mota kamar yadda akayi"

"Allah ne kawai ya tsirar da mu baki daya" inji dan majalisan.

Ya cigaba da cewa "Yan sandan duk tsere wa sukayi a yayin da yan boko haram suka bude musu wuta, abin dai babu dadin gani"

"Bayan yan sandan sun gudu kuma direban da ke tuka motar da matan suke ya guda, yan boko haram din suka tafi da matar a motan, mu dai abin da ya tsirar da mu shine masu tsaro da ke gaban mu sun sunyo reverse sun tarwatsa mayakan boko haram din"

Dan majilisan ya bada shawarar cewa jami'an tsaro ya kamata su bi yan boko haram har cikin daji su yake su ba wai su rika jira sai an kawo farmaki ba kafin su kare kansu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel