Yan Boko Haram sunyi kwanton bauna sun farwa matafiya a hanyan Maiduguri

Yan Boko Haram sunyi kwanton bauna sun farwa matafiya a hanyan Maiduguri

Rahotanni daga kafafen yada labarai sun bayyana cewa wasu da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne, sun kai harin kwanton-bauna a kan ayarin motocin da ke hanyar Maiduguri zuwa Damboa a jihar Borno ranar Talatar da ta gabata, duk da cewa ayarin na tare da rakiyar sojoji kamar yadda aka saba.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Borno Damien Chukwu, ya tabbatar da mutuwar dan sanda daya da kuma direban wata mota.

NAIJ.com ta samu labarin cewa sai dai shaidu sun ce adadin zai iya zarta haka, idan aka yi la’akari da cewa akwai wasu jami’an ‘yan sanda akalla 63 daga cikin ayarin bayan an canza masu wurin aiki.

Yan Boko Haram sunyi kwanton bauna sun farwa matafiya a hanyan Maiduguri

Yan Boko Haram sunyi kwanton bauna sun farwa matafiya a hanyan Maiduguri

Akalla motoci 200 ne a cikin ayarin da ke tafiya, inda wata mota kirar Bus mai daukar mutane 80, ke dauke da ‘yan sandan da aka yi wa canjin aiki daga Oghara na jihar Delta zuwa Askira Uba.

Wata majiya ta ce an dauki lokaci ana musayar wuta tsakanin mayakan da Jami’an tsaro, daga bisani kuma jiragen yaki su ka kai dauki.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel