YANZU-YANZU: Yan sandan Najeriya sun gano wasu muggan makamai a cikin bola

YANZU-YANZU: Yan sandan Najeriya sun gano wasu muggan makamai a cikin bola

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Anambra ta bayyana cewa ta gano makamai masu tsatsa 14 da kuma iwasfar harsashi 2 a cikin wani rami kusa wurin zubar da shara a Uruagu Nnewi, a karamaar hukumar Nnewi ta kudu a jihar Anambra.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Sam Okaula ya bayyana hakan ne a wani zama na musamman da yayi da manema labarai, inda ya ce an gano makaman ne a yayin da ‘yan bola suke gina rami a wurin.

NAIJ.com ta samu labarin cewa ya ce makaman da aka gano ba su da alaka da babban motan da aka kama wanda ya fito daga Arewancin kasa cike da doya da makamai da kuma harsashi.

YANZU-YANZU: Yan sandan Najeriya sun gano wasu muggan makamai a cikin bola

YANZU-YANZU: Yan sandan Najeriya sun gano wasu muggan makamai a cikin bola

Ya kuma nuna bacin ran sa game da masu amfani da yanar gizo wajen baza labarun karya mara sa kyau wanda yawanin su karya ne a shafi daban daban a yanar gizo.

Okaula yayi kira ga al-ummah da su gujewa wannan harkar.

Ya kuma dauki alkawarin yaki da ta’addanci a jihar domin ganin an samu zaman lafiya a duk fadin jahar, inda yayi kira al-umma mazauna Anambra da su bada hadin kai ga jami’an tsaro na ‘yan sanda wajen tona asirin bata gari.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel