Kwamacala: Yan sanda sun cafke wata mata bisa zargin sace saurayin ta dan shekara 17

Kwamacala: Yan sanda sun cafke wata mata bisa zargin sace saurayin ta dan shekara 17

- Wata mata ‘yar shekara 26 mai suna Oluchi Paul a ranar Laraba ta bayyana a gaban kotun Majistare da ke Ikeja a kan zargin sace wani dan matashi.

- Wadanda ake zargi ‘yar kasuwa ce wace ke zama a gida mai lamba 6, Yunusa Lane, Water Works da ke unguwan Iju, a ta wajen garin Legas, ana cajin ta da aikata laifuka guda 3 wadanda suka hada da satan mutum.

NAIJ.com ta samu labarin cewa wanda ya mika karan zuwa kotu, Sufeto Clifford Ogu, ya bayyana ma kotu cewa laifukan da wanda ake zargi ta aikata ta aikata su ne tun a watan Maris zuwa Mayu 2017 a gidan ta.

“Wanda ake zargi ta sace wani matashi dan shekara 17 domin ta rinka saduwa da shi.

“Iyayen yaron suna ta neman yaron su sai aka ba su labarin cewa ai dan su na wurin ita wannan matan a gidan ta.

Kwamacala: Yan sanda sun cafke wata mata bisa zargin sace saurayin ta dan shekara 17

Kwamacala: Yan sanda sun cafke wata mata bisa zargin sace saurayin ta dan shekara 17

“Iyayen wanda aka wa rauni suka kai karan lamarin zuwa ofishin ‘yan sanda.

“Yan sanda kuma tafi gidan wadda ake zargi inda suka same ta tare da yaron a gidan ta,” Ya ce.

Ogu ya ce tuni ‘yan sanda suka kama wadda ake zargi da yaron zuwa ofishin domin a masu tambayoyi.

“Ita wadda ake zargi ta gayawa ‘yan sanda cewa ita da yaron masoya ne sannan kuma a yanzu haka tana dauke da juna biyu wanda yaron ne uban.,” Ya ce.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel