Hawan Osinbajo ya sa matsalar fasa bututun mai ya ragu da kashi 12

Hawan Osinbajo ya sa matsalar fasa bututun mai ya ragu da kashi 12

Rahotanni sun daga Kamfanin matatar man fetur na Nijeriya NNPC, sun bayyana cewa an samu raguwar fasa bututun mai da sama da kashi 12 cikin 100, biyo bayan matakan da gwamnatin tarayya ta dauka na sanya masu ruwa da tsaki a kan hanyoyin da za a bi domin shawo kan matsalar.

Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin rahoton wata-wata na aikace-aikacen kamfanin da aka fitar na watan Afrilu na shekara ta 2017 a Abuja.

Hawan Osinbajo ya sa matsalar fasa bututun mai ya ragu da kashi 12

Hawan Osinbajo ya sa matsalar fasa bututun mai ya ragu da kashi 12

NAIJ.com ta samu labarin cewa ya ce fasa bututun mai na karkashin kasa ya ragu daga kashi 94 zuwa 82 a watan Maris, an kuma kara samun raguwar sa a cikin watan Afrilu.

A bangaren aikace-aikacen kamfanin kuwa, ya ce an samar da litocin man fetur kimanin billiyan daya da dubu dari 2 a cikin kwanaki 34.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel