Amurka zata taimakawa Najeriya ta ci gaba da zama kasa daya

Amurka zata taimakawa Najeriya ta ci gaba da zama kasa daya

- Jakadan kasar Amurka a Najeriya ya bayyana cewa kasarsa ashirye take ta taimakawa Najeriya domin ta ci gaba da zama kasa daya

- Jakadan yace ya ziyarci jihohin Oyo da Osun dake kudu maso yammacin Najeriya domin ya kara fahimtar kasar

- Gwamnan jihar Osun ya bukaci kasar Amurka ta kara mayar da hankali ga jagorancin kasashen duniya domin hana ta wargajewa

Kasar Amurka ta ce ashirye take ta taimakawa Najeriya a fannoni daban-daban ciki har da raya kasar da kokarin da shugabannin kasar keyi domin tabbatar da cewa kasar ta ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya.

Jakadan Amurka a Najeriya ya furta hakan a ziyarar da ya kai wa gwamnan jihar Osun Abdulrauf Aregbesola a birnin Osogbo fadar gwamnatin jihar Osun dake kudu maso yammacin Najeriya.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, jakadan ya ce Najeriya nada mahimmanci a wajen ci gaban kasashen duniya inda ya kara da cewa kasarsa zata ci gaba da taimakawa Najeriya a duk hanyoyin da suka dace domin ta ci gaba. Ya ce hadin kai nada amfani ga kowace al'umma a duk fadin duniya. Saboda haka hadin kan Najeriya nada amfani sabili da haka ne ya ziyarci jihar domin kara fahimmatar kasar.

Amurka zata taimakawa Najeriya ta ci gaba da zama kasa daya

Shugaban kasar Amurika, Donald Trump

KU KARANTA: Osinbajo zai gana da gwamnoni 36 kan batun Bayafara

Yayin da yake yiwa Jakadan maraba, lale, gwamna Aregbesola ya ce suna jin dadin jagorancin da Amurka ke yiwa kasashen duniya don haka kasar ta Amurka ta kara mayar da hankali ga jagorancin domin hana kasashen duniya wargajewa.

Kafin ya isa jihar Osun sai da Jakadan na Amurka ya ziyarci jihar Oyo inda ya sake jaddada matsayin Amurka a kan taimakawa Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yaya zaku ji idan Donald trump ya ce zai durkushe Boko Haram kamar yanda ya yi a kasar Siriya?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel