Dandalin Kannywood: Ina so a sanni duka duniya - Rahma Sadau

Dandalin Kannywood: Ina so a sanni duka duniya - Rahma Sadau

- Rahma Sadau ta dawo fim tun bayan da kungiyar Moppan ta kore ta daga kannywood. Bisa wata waka da suka yi ita da mawaki Classiq.

- Bayan Jaruma Rahma Sadau ta bayar da hakuri akan laifin da ta aikata.

- Kungiyar Moppan ta sanarwa duniya cewa ta dawo da jaruma Rahma Sadau Kannywood.

NAIJ.com ta samu labarin cewa jarumar ta bayyanawa jaridar Premium Time cewa: "Dawowa ta kungiyar kannywood ba zai hanani yin fina finan kudanci ba (nollywood). Domin cikar jaruma shine a santa aduniya."

Acewar Rahma Sadau: "Ni dama burina in zama jaruma ta duniya gaba daya, ba kawai jaruma a hausa fim ba. Misali, Ali Nuhu da Sani Danja matsayinsu nake so in kai a harkar fim. Ba wai kudi ko wata kadara ba, a'a, kawai a san ni aduniya kamar yanda aka san su.

Dandalin Kannywood: Ina so a sanni duka duniya - Rahma Sadau

Dandalin Kannywood: Ina so a sanni duka duniya - Rahma Sadau

Kuma duk suna yin fina finan kudanci, dan haka ba gurin sunan su Ali Nuhu da sani danja basu shiga ba. Nima haka nake so in zama. Inji Rahma Sadau.

Zata ci gaba da yin fim na kudanci inji Rahma Sadau.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel