Atiku ya fara shirin fafatawa da Sule Lamido a takarar shugaban ƙasa 2019

Atiku ya fara shirin fafatawa da Sule Lamido a takarar shugaban ƙasa 2019

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar zai yi takara a 2019

- Shima tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya nuna sha'awarsa

An fara shirin mummuke tsakanin tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakara dangane da zabukan 2019.

Jaridar New Telegraph ta ruwaito giwayen siyasan guda biyu sun fara kafa turakan da zasu taimaka musu wajen share kafar juna a zabukan na 2019.

KU KARANTA: Yansanda sun kama Uba da ɗa, da hannu cikin kisan jigon APC (Hotuna)

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito cewa “Atiku ya yarda tsagin Tinubu, inda ya rungumi kungiyar yarbawa Afenifere tare da wasu tsofaffin gwamnonin yankin kudu maso yammacin kasar nan dayake ganin zasu mara masa baya.

Atiku ya fara shirin fafatawa da Sule Lamido a takarar shugaban ƙasa 2019

Atiku da Sule Lamido

Sai dai ana ganin idan Makarfi ya samu nasara a kotun koli, toh Atiku ka iya komawa jam’iyyar PDP don yin takarar shugaban kasa.

Amma duk da wadannan hasashe irin na siyasa, Sule Lamido ma ba kanwar lasa bane, inda tuni ya ayyana sha’awarsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2019, hakan ya sanya lallai sai Atiku Abubakar ya zage damtse kafin ya iya kalubalantar Lamido.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel